Bakori, Jihar Katsina – 11 ga Nuwamba, 2025
An kai wani sabon hari daga ‘yan bindiga a garin Bakori, inda suka yi nufin sansanin Fulani da ke bayan Sakatariyar Karamar Hukuma, wanda aka fi sani da Gandun Sarki, da yammacin ranar Litinin.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace dabbobi da dama, sannan suka yi musayar wuta da jami’an tsaro yayin da suke kokarin tserewa. A yayin musayar wutar, ɗan sanda ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu biyu suka ji raunuka. Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu daga cikin ‘yan bindigar an kashe su.
Wasu ganau daga cikin Kungiyar Hulɗar Jama’a da ‘Yan Sanda (PCRC), wadanda suka yi magana a sharadin rashin bayyana sunayensu, sun shaida cewa ‘yan bindigar sun bayyana tun da yammacin ranar suna hawa babura kusan 43, kusan mutane uku-uku ne ke kan kowanne babur, dauke da bindigogi yayin da suke tafiya zuwa Bakori. Mutanen Bakori sun bayyana cewa suna sauraron yadda ‘yan bindigar ke magana a oba-oba (walkie-talkie) cikin Fillanci yayin da suke tsara harin.
Wannan sabon hari ya zo ne kasa da wata guda bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ƙananan hukumomi biyar a Kudancin Katsina, ciki har da Bakori. Sai dai, yayin da wasu yankuna suka samu sassaucin tashin hankali, Bakori na ci gaba da fuskantar hare-hare akai-akai.
Wasu masu lura da al’amura sun danganta wannan sabon hari da ƙin amincewar wasu ‘yan bindiga shiga yarjejeniyar zaman lafiya gaba ɗaya, duk da ƙoƙarin da ake yi na tattaunawa da sulhu.
Shugaban al’umma kuma masani kan harkokin tsaro, Mahadi Danbinta Guga, ya bayyana takaicinsa kan yadda yarjejeniyar zaman lafiya ta gaza haifar da sakamako mai dorewa.
A cikin wata wallafa a shafinsa na Facebook, Mahadi ya rubuta:
“Ba sai ka zama mai adawa, mai ƙyamar gwamnati ko mai tsanani ba kafin ka fahimci cewa yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a Bakori ta zama tarihi!
Karamar hukumar ta samu kwanciyar hankali na kwanaki biyu kacal bayan yarjejeniyar. Tun daga nan, hare-hare sun ci gaba inda rayuka da dukiyoyi suka salwanta, mutane suka ji rauni ko aka yi garkuwa da su, aka sace dabbobi, kuma al’umma ta shiga cikin damuwa da tashin hankali.
A jiya Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, an kai hari kan sansanonin Fulani guda biyu — Rugar Alhaji Lawal da Saleh a Layin ’Yannehu, Guga Ward — inda aka sace dabbobi. Haka kuma an kai hari a Gidan Kaɗo, aka yi awon gaba da dukiyoyi. Garin Bakori kansa bai tsira ba; an kai masa hari a Gandun Sarki, amma gaggawar haɗin guiwar jami’an tsaro ce ta hana mummunan bala’i.
Muna matuƙar godiya ga rundunar Sojojin Sama, Sojojin Ƙasa, ‘Yan Sanda, da vigilante da suka haɗa kai suka fatattaki maharan."
Mazauna yankin sun sake roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara ƙoƙari wajen kai dauki da kuma sake nazarin yarjejeniyar zaman lafiya domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Bayani:
Wannan rahoto ya dogara ne akan bayanan mazauna yankin da kuma rubuce-rubucen shugabannin al’umma a kafafen sada zumunta. Har yanzu ba a samu tabbacin hukumomin tsaro ba a lokacin da ake wallafa wannan rahoto.
Tags
Sabbin Labarai