Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan
Katsina, Lahadi, 10 ga Nuwamba, 2025
An rage kudin kujerar aikin Hajjin 2026 ga mahajjatan Jihar Katsina da sauran jihohin Arewacin Najeriya zuwa Naira Miliyan 7.67, bisa sabuwar sanarwar Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON).
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya bayyana hakan cikin wata hira da DCL Hausa daga kasar Saudiyya, inda ya ce rage kudin ya zama dole ne bayan amincewar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da bayar da tallafi don rage nauyin kudi ga masu niyyar zuwa hajji.
Farfesa Pakistan ya ce, hakan kuma ya biyo bayan tattaunawa ta baya-bayan nan da hukumar ta yi da kamfanonin masu samar da hidimomi daga Saudiyya.
A karkashin sabon tsari, jihohin da ke yankin Borno da Adamawa za su biya Naira 7,579,020, yayin da mahajjatan Katsina da sauran jihohin Arewa za su biya Naira 7,669,769. Daga bangaren jihohin Kudu kuwa, za su biya Naira 7,991,141, sabanin Naira 8,784,085 da aka sanar a baya.
Shugaban NAHCON ya ce wannan ragin kudin ya nuna kokarin gwamnati na saukaka wa alhazai domin karin halarta a aikin Hajjin bana.
A karshe, hukumar ta kayyade ranar 5 ga watan Disamba, 2025, a matsayin ranar karshe ta biyan kuɗin Hajji ga duk masu niyyar tafiya. NAHCON ta shawarci masu niyyar zuwa su kammala biyan kuɗinsu kafin wannan lokaci domin tabbatar da samun kujerarsu.
Tags
Sabbin Labarai