RAHOTO NA BINCIKE: Almundahana, Son Kai da Cin Hanci a Hukomomin Ilimin Kananan Hukumomi (LEAs) na Jihar Katsina — Malamai na Cikin Wahala Yayin da Cin Hanci ke Kara Rarrafe


Daga Wakilanmu | Jihar Katsina –
Binciken da wakilanmu suka gudanar ya tona asirin wata babbar barna da ake yi ta lokaci mai tsawo a cikin Hukomomin Ilimin Kananan Hukumomi (LEAs) a fadin Jihar Katsina — lamarin da ya zarce abin da aka fara haskawa a Karamar Hukumar Bakori.

Abin da ya fara a matsayin rahoto kan cire albashi da cin zarafin malamai a LEA ta Bakori, ya zamo hanya ta gano munanan abubuwa da suka wuce tunani. Binciken ya nuna cewa wannan matsala ba ta takaita ga Bakori ba — kusan dukkan LEAs a jihar na fama da makamanciyar matsala, har da wasu Kananan Hukumomin kansu.

Rashin Biyan Albashi: Matsala da ta Yadu

Malaman makaranta daga LEAs daban-daban ciki har da Bakori, Batagarawa, Funtua, Kankia, Malumfashi, Jibiya da Daura sun tabbatar da cewa ana hana su albashi ba tare da wani bayani ba. Da yawa daga cikinsu na shafe watanni ba tare da samun albashinsu ba, kuma ko da an dawo da biyan albashin, ba a taba maido musu da kudin da suka rasa ba.

Mummunan abin damuwa shi ne irin wannan abin yana faruwa a wasu Kananan Hukumomi ma, inda ake hana ma’aikata albashi ko a canza adadin ba bisa ka’ida ba.

“Abin yana kamar caca ne — ba ka san ranar da za a hana ka albashi ba ko ko da za ka samu cikakke,” in ji wani malami daga Jibiya da ya nemi a sakaya sunansa.

Almundahanar Daukar Ma’aikata: Ma’aikata na bogi da Madadin Malamai

Binciken ya gano wata mummunar dabara da ke gudana yadda mata malamai da suka bar jihar don su zauna tare da mazajensu a wasu sassa na kasar, ke ci gaba da karɓar albashi. Wadannan malamai na amfani da marasa aikin yi wajen koyarwa a madadinsu, suna biyansu ‘yan kuɗi — kuma wannan tsari na faruwa ne da sanin wasu jami’an LEA.

Bugu da ƙari, akwai malamai da dama da suka bar aikin gwamnati don komawa aiki da gwamnatin tarayya ko wasu kamfanoni masu zaman kansu, amma har yanzu suna cikin jerin masu albashi a LEA. Wadannan ‘ma’aikatan bogi’ sukan bayyana ne kawai lokacin tantance ma’aikata don tabbatar da sunan su na cikin jerin.

Sayar da Karin Girma

Wani ɓangare mai tada hankali da binciken ya bankado shi ne yadda ake sayar da karin girma (promotion). Malamai daga LEAs daban-daban sun tabbatar cewa an daina bai wa ma’aikata karin girma bisa cancanta ko shekara, sai dai ga wanda ya iya biya.

“Lokacin da sakon karin girma ya fito, sai an biya kafin a baka,” in ji wani malami daga BLEA Bakori. “Wanda bai da kudin biya, zai ci gaba da zama a matsayinsa na shekaru da dama.”

Son Kai, Rashin Adalci da Cin Zarafi a Harkokin Gudanarwa

Binciken ya kara gano yadda ake fifita ‘yan uwa da abokai a cikin makarantun firamare. A wasu makarantu, malamai a matakin Grade Level 10 ko 12, har ma da 9, ana nada su shugabannin makarantu, yayin da manyan malamai da ke Grade Level 13 ko 14 ke zama a ƙarƙashinsu.

“Wannan tsarin na haifar da rashin jin daɗi da raguwar kwarin gwiwa,” in ji wani babban malami daga Bakori. “Komai dangantaka da wanda ka sani ne.”

Zaɓen malamai da ake turawa tarurruka ko horo (workshops) ma bai da adalci — ana ɗaukar na kusa da shugabanni ne kawai, yayin da waɗanda suka cancanta ke ci gaba da zama a gefe. Rahotanni sun nuna cewa abincin da ake ba mahalarta tarukan yawanci bai kai matakin da ya dace ba duk da kasafin kudin da ake warewa.

Kiran Gudanar da Bincike a Fadin Jiha

Yanzu da irin wannan cin zarafi ya bayyana fili, masu ruwa da tsaki da masana harkar ilimi na kira ga Gwamna Malam Dikko Umaru Radda da ya faɗaɗa bincikensa fiye da Bakori kaɗai.

“Gwamna ya kamata ya jefa komar bincikensa gaba daya,” in ji wani tsohon jami’in ilimi. “Ba kan wata Karamar Hukuma guda abin ya tsaya ba. Dukkan tsarin ya samu tabo, kuma sai dai sauyi nagari ne zai kawo sauki.”

Malamai a fadin Jihar Katsina na ci gaba da shan wahala sakamakon wadannan matsaloli — an hana su haƙƙinsu, an zalunce su, an kuma raunana su. A yayin da jihar ke fuskantar ƙalubale na tattalin arziki da hauhawar rashin aikin yi, buƙatar gaskiya, adalci da gyara a harkar ilimi ba ta taɓa zama dole fiye da yanzu ba.

Ƙoƙarin da ake yi na samun amsa daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Katsina da Hukumar SUBEB na ci gaba da gudana, yayin da jama’a ke ƙara matsa lamba.

An samo labarin daga Katsina Times 

Ahmed Abdulkadir

I am a Broadcast Regulator, based in Katsina. I retired as the Zonal Director, National Broadcasting Commission, Maiduguri Zone. I earned a Master's in Development Studies from Bayero University, Kano, Nigeria; a Bachelor of Education in Language Arts from Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria; a Nigeria Certificate in Education; a Diploma in Journalism; a Certificate in Communication Research and a Certificate in Radio Journalism and Management.

Post a Comment

Previous Post Next Post