Gwamnatin Jihar Katsina Zata Ɗauki Malaman S-Power 7,000 Aikin Malanta na Dindindin

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Faruk Lawal Joɓe


Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana shirinta na daukar karin malaman makaranta 7,000 a fadin jihar. Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon Faruq Lawal Jobe ya sanar da hakan a lokacin da yake kaddamar da mambobin kwamitin da za su tantance wadanda za a dauka din a ofishinsa, a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuli, 2023.

Mataimakin Gwamnan ya ce za a dauki malaman makaranta 5,000 dake da shaidar malanta ta kasa NCE/Diploma da za su koyar a makarantun firamare da kuma 2,000 masu digiri da za su koyar a makarantun sakandare na jihar.

Kazalika, mataimakin Gwamnan ya ce kwamitin zai yi bita kan sabuwar daukar malaman makaranta 3,889 da aka dauka karkashin hukumar kula da ilmin firamare ta SUBEB, inda ya ce za a sake tantance su tare da jarabawa domin tabbatar da ba a yi kitso da kwarkwata ba.

Hon Faruq Lawal Jobe ya yi bayani gamsasshe game da yadda shirin daukar aikin zai kasance.

Tun da farko, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Arch Ahmad Musa Dangiwa ya gabatar da mambobin kwamitin da kuma kamfanin kwararri da zai shirya jarabawa ga wadanda za a dauka aikin. Arch Ahmad Musa Dangiwa ya bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tsakani ga Allah ba tare da nuna son rai ba.

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Ahmad Musa Ɗangiwa


Kwamitin dai na da Dr Sabi'u Dahiru a matsayin shugaba sai Malam Lurwanu Haruna Gona a matsayin Sakatare.

Sauran mambobin kwamitin su ne Malam Shamsudden Sani, Dr Isah Idris Zakari, Mannir Ayuba Sullubawa, Shehu Abdullahi Mohammed da Zakariya'u Musa Doka. Kwamitin na da wata daya ya gabatar da rahotonsa.

Ahmed Abdulkadir

Ahmed Tijjani Abdulkadir is a seasoned media executive, journalist, teacher, entrepreneur, and public servant with over 35 years of distinguished experience in broadcasting, media regulation, public communication, and education. He currently serves as the Chairman of the Katsina State Radio and Television Service Board and holds several leadership positions in the private sector. He is the Chairman of Namowa MediaHub and Barau & Namowa Agro-Allied and General Services, as well as the Managing Director of Broadsphere Ventures Limited and Managing Director of FASAB Foods Nigeria Ltd. Mr. Abdulkadir holds a Master’s degree in Development Studies from Bayero University, Kano, and a Bachelor of Education (Language Arts) from Ahmadu Bello University, Zaria. He also possesses professional qualifications in journalism and broadcasting from the International Institute of Journalism (IIJ) Abuja, NTA Television College Jos, and The Thomson Foundation/British Council, and a Certificate in Digital Journalism (Reuters/Meta Journalism Project).

Post a Comment

Previous Post Next Post