INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da ƴan majalisun jihohi da mako ɗaya

Shugaban Hukumar Zaɓen Nigeria, INEC, Prof. Mahmud Yakubu 

Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris

INEC ta tabbatar wa da BBC ɗage zaɓen, bayan wani taron gaggawa da manyan jami'an hukumar suka yi a Abuja.

Kafofin yaɗa labarai na Najeriya sun ambato cewa INEC ba ta kammala saita 'tantance masu zaɓe ba ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabirairu.

Sun ƙara da cewa hukumar ta ce sai ta samu damar kwashe bayananta da ta tattara na a yayin zaɓen shugaban ƙasar zuwa wani rumbunta na daban kafin ta sake saita na’urar ta yadda za a yi zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da wata damuwa ba.

Tun da farko, an tsara gudanar da zaɓen ne a ranar asabar 11 ga watan Maris.

Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan wata kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta amince da buƙatar hukumar zaɓe ta ƙasar ta sake saita na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaɓen shugaban ƙasar.

Tawagar alƙalan kotun mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin Joseph Ikyegh ta yanke hukuncin cewa an bai wa INEC damar ne domin gudanar da zaɓen gwamnoni wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 11 ga watan Maris tun da fari.

Hukuncin na nufin kotun ta ƙi amincewa da buƙatar da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP Peter Obi ya shigar ta neman hana INEC goge bayanan masu zaɓen da aka naɗa a zaɓen shugaban ƙasar.

Tawagar alƙalan ta ce INEC ta bayyana cewa tana da shirin kwashe bayannan da ke cikin na'urar 176,000 da aka yi amfani da su a zaɓen ta wallafa su a wani rumbun bayananta na daban, ko da yake Obi da LP ba su nuna ƙin amincewa da wannan shiri ba.

Ahmed Abdulkadir

Ahmed Tijjani Abdulkadir is a seasoned media executive, journalist, teacher, entrepreneur, and public servant with over 35 years of distinguished experience in broadcasting, media regulation, public communication, and education. He currently serves as the Chairman of the Katsina State Radio and Television Service Board and holds several leadership positions in the private sector. He is the Chairman of Namowa MediaHub and Barau & Namowa Agro-Allied and General Services, as well as the Managing Director of Broadsphere Ventures Limited and Managing Director of FASAB Foods Nigeria Ltd. Mr. Abdulkadir holds a Master’s degree in Development Studies from Bayero University, Kano, and a Bachelor of Education (Language Arts) from Ahmadu Bello University, Zaria. He also possesses professional qualifications in journalism and broadcasting from the International Institute of Journalism (IIJ) Abuja, NTA Television College Jos, and The Thomson Foundation/British Council, and a Certificate in Digital Journalism (Reuters/Meta Journalism Project).

Post a Comment

Previous Post Next Post