An Ƙaddamar Da Kwamitocin Miƙa Mulki A Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari 

Daga Katsina Post 

Gwamna Aminu Bello Masari ya ƙaddamar da kwamitocin miƙa mulki ga sabuwar Gwamnatin jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin zaɓaɓɓen Gwamnan jihar, Dr. Dikko Raɗɗa.

A ranar 18 ga watan Maris a ka gudanar da zaɓen Gwamna a jihar Katsina wanda Dr. Dikko Raɗɗa ya lashe zaɓen ƙarƙashin jam'iyyar APC, za'a kuma miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun bana. 


Sakakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal, shi ne zai jagoranci kwamitin miƙa mulkin mai membobi 40 sai kuma Kwamishinan Ruwa da albarkatu,  Musa Adamu Funtua, shi ne zai jagoranci kwamitin shirye-shirye da tsare-tsare, wanda ke ɗauke da membobi 43. 


Da ya ke jawabi yayin ƙaddamarwar, Masari ya yi kira ga Kwamitocin da su yi aikin tuƙuru don ganin an cimma nasarar miƙa mulki kamar yanda a ka tsara. 

Sannan ya roƙi Allah da ya ba kwamitocin damar aiwatar da aikin su don al'ummar jihar Katsina su cigaba da cin gajiyar mulkin jam'iyyar APC da ke tabbatar da romon damokaraɗiyya.

Ahmed Abdulkadir

Ahmed Tijjani Abdulkadir is a seasoned media executive, journalist, teacher, entrepreneur, and public servant with over 35 years of distinguished experience in broadcasting, media regulation, public communication, and education. He currently serves as the Chairman of the Katsina State Radio and Television Service Board and holds several leadership positions in the private sector. He is the Chairman of Namowa MediaHub and Barau & Namowa Agro-Allied and General Services, as well as the Managing Director of Broadsphere Ventures Limited and Managing Director of FASAB Foods Nigeria Ltd. Mr. Abdulkadir holds a Master’s degree in Development Studies from Bayero University, Kano, and a Bachelor of Education (Language Arts) from Ahmadu Bello University, Zaria. He also possesses professional qualifications in journalism and broadcasting from the International Institute of Journalism (IIJ) Abuja, NTA Television College Jos, and The Thomson Foundation/British Council, and a Certificate in Digital Journalism (Reuters/Meta Journalism Project).

Post a Comment

Previous Post Next Post